'Za a dau wata shida kafin a shawo kan Ebola'

Image caption Ana daukar Ebola ne ta jini da ruwan da ya fito daga jikin wanda ya kamu da ita da kuma gawa

Kungiyar agaji ta Likitoci ta Medecins Sans Frontieres ta ce zai dauki tsawon watanni shida masu zuwa kafin a shawo kan barkewar cutar Ebola a Yammacin Afrika.

Shugabar kungiyar, Joanne Lui ta yi kira da kasashen duniya su kara hada karfi waje guda karkashin jagorancin Hukumar lafiya ta Duniya, domin tunkarar cutar.

Ta kara da cewa shawo kan cutar ta Ebola a kasar Liberiya inda aka samu mutuwar fiye da mutane 300 na da matukar muhimmanci wajen magance barkewar annobar ta Ebola.

"Dole ne gwamnatoci su dauki matakai a halin yanzu, idan har muna son mu kawo karshen annobar" A cewar Ms Lui