An kai wa shafin twitter na Medvedev hari

Masu satar bayanai sun shiga cikin shafin twitter na Firaministan Rasha Dmitry Medvedev jiya alhamis inda suka sa wani sako da ya ce ya yi murabus.

Shafin wanda kuma ke da magoya baya miliyan biyu da rabi , ya rika samun sakonin da suka yi Alla wadai da shugaba Vladimir Putin.

Masu satar bayanai sun rubuta cewa Mr Medvedev zai maida hankali akan sabuwar sana'arsa ta daukar hoto.

Hakkin mallakar hoto Getty

Wani gungu masu satar bayanai a Rasha ya dauki alhakin kai harin.

Gwamnatin kasar ba ta bata lokaci ba wajen tabattar da lamarin.

"Na ajiye mukami na, ina takaici akan matakan da gwamnati ta dauka, a yi man afuwa, a cewar masu satar bayanai da suka shiga cikin shafin twitter na Medvedev.

Hakkin mallakar hoto AFP

Kungiyar mai suna Shaltay Boltay ta kuma yi ikirarin shiga cikin shafin Google da kuma wayar tafi da gidanta watau Iphone na Firaministan kasar.

Tun bayan da kungiyar Shaltay Boltay ta bayana a watan disemba bara take tasiri wajen satar bayanan mahukuntan kasar .

Ta wallafa bayanan fadar kremlin ciki har da jawabin sabuwar shekara na shugaba Vladimir Putin a shekarar da ta gabata.

Haka kuma a makon daya gabata Shaltay Boltay ta wallafa sakonin email na sirri na shugaban sashin dake sa ido akan shafukan shugaban kasa