Ebola: Kenya ta hana 'yan wasu kasashen Afrika shiga kasarta

Yaki da cutar ebola Hakkin mallakar hoto science photo library
Image caption Yaki da cutar ebola

Bayan barkewar cutar ebola mai kisa a wasu kasashe na Afrika ta Yamma, hukumomin lafiya a Kenya sun haramta wa 'yan kasashen da cutar ta fi yi wa barna kai ziyara kasar Kenyar.

Babban sakatare a ma'aikatar lafiya ta kasar Kenyar James Macharia ya ce sun dauki matakin ne na wucingadi, domin kare lafiyar jama'a.

Sai dai ya ce za a kyale 'yan kasar Kenyar dake komawa gida daga kasashen na Guinea, da Liberiya, da kuma Saliyo, koda kuwa sun kamu da cutar.

Kampanin zirga zirgar jiragen saman Kenya Airways , ya ce zai dakatar da zirga zirga zuwa Saliyo da Liberiya saboda barkewar cutar ebolar.

Dakatarwar zata fara aiki ne daga sha biyun daren ranar Talata.

Jirage zasu ci gaba da zirga zirga tsakanin Kenyar da Nijeriya.