An kai hari a cibiyar Ebola a Liberia

Unguwar West Point a Manrovia Hakkin mallakar hoto Getty

Rohotanni daga Laberiya na cewa wasu mutane sun farma wani wuri da aka kebe mutanen da suka nuna alamun cutar Ebola inda suka sace kayan mutanen da aka kebe.

Cikin kayan da ake sace harda zanin gado da katifun masu jinyar.

Abunda ya sa mutane fargabar cewa cutar zata iya yaduwa.

Wakilin BBC a Manrovia ya ce: "Mutanen unguwar na nuna damuwar cewa saboda wasu daga cikin katifun da mashinfidun da aka sace nada jini-jini da amai a jikin su, to cutar zata iya yaduwa a unguwar wadda can dama mutanen ta na fama da talauci.

Rohotanni sun nuna cewa mutanen da suka kai harin kan sansanin Ebolan na nuna takaicin su ne saboda kafa cibiyar a unguwar su batareda tuntubar su ba.

Yanzu haka an kai Kimamnin mutane 30 dake sansanin, zuwa Asibitin JF Kennedy, wanda shine mafi girma a kasar, inda ake da wuri na musanan na yiwa masu fama da Ebola Magani.

Hakan na nufin kenan sanansanin na West Point zai dena aiki. Sai dai ko idan gwamnati zata sasanta da mutanen unguwar don kafa wani sanansani da iznin su

Karin bayani