Ebola: Maganin Nano Slyer zai taimaka inji Agwale

Wani mutum dake fama da cutar Ebola
Image caption Wani mutum dake fama da cutar Ebola

Mutumin daya kawo maganin Nano Slyver a Najeriya Dakta SimoN Agwale ya ce yana da yakinin maganin zai taimaka sosai wajen yaki da cutar.

Hukumomin lafiya a Najeriya sun ce za su yi bincike kafin suyi amfani da maganin Nano-Sylver akan masu fama da cutar Ebola a kasar.

Dakta Agwale ya ce ko da yake ba a taba gwada maganin akan masu fama da cutar Ebola ba, maganin na Nano-Sylver ya dade ana amfani da shi akan wasu cututtuka da sukafi kwayar cutar Ebola karfi, kuma yayi tasiri.

Hukumar kula da abinci da magunguna ta kasar Amurka, ta yi gargadi akan hadarin amfani da ko wanne irin magani akan masu fama da cutar ta Ebola, a dai dai lokacin da gwamnatin Najeriyar ta ba da damar a kai mata Nano-Sylver.