Imran Khan na zaman dirshan Pakistan

Imran Khan Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Imran Khan

Wani fitaccen dan hamayyar siyasa a Pakistan, Imran Khan ya ce zai ci gaba da zaman dirshan a titunan Islamabad, babban birnin kasar, shi da magoya bayansa har sai FiraMinista Nawaz Sharif ya sauka daga mukaminsa.

Lokacin da yake jawabi ga dubban magoya bayansa, Imran Khan ya zargi Firaminista Shariff da aikata magudi a zaben 2013.

Lokacin da yake jawabi a wani taron gangamin na daban a birnin, wani dan siyasar, Tahirul Qadri yayi kiran da a dauki matakan kifar da gwamnati amma ba tare da tashin hankali ba.

Gwamnatin dai ta ce a shirye take ta gudanar da bincike kan zargin magudi, amma ba za a sauke Mr Sharif ta hanyar gangami ba.