Fafaroma na ziyara a Seoul

Hakkin mallakar hoto

Fafaroma Francis ya yi kira ga malaman darikar Katolika da su kasance masu kaskantad da kai, yana mai cewa, wadanda ke ambaton talauci a baka, amma suke rayuwa cikin daula, munafukai ne, dake zubar da mutuncin cocin da kuma sakon da yake son isarwa.

Fafaroman wanda ke ziyara a Koriya ta Kudu, ya bayyana hakan ne a wata cibiyar tsugunar da masu fama da rashin lafiya da kuma nakasa, wadda wani fadan cocin ya kafa shekaru talatin da takwas da suka wuce.

Addu'o'in wasu mabiya Kotolikan kenan a Seoul, babban birnin kasar, lokacin da Fafaroman ya halarci taron addu'o'i ga wasu 'yan kasar Korean su dari da ashirin da aka kashe.

Lamarin ya faru ne shekaru dari biyu da suka wuce kan kasancewarsu mabiya cocin.