An hana Rolf Buchholz shiga Dubai

Rolf Buchholz, mutumin da aka fi yi ma huji a duniya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rolf Buchholz, mutumin da aka fi yi ma huji a duniya

Hukumomi a Dubai sun hana wani mutumin kasar Jamus shiga birnin. Mutumin mai suna Rolf Buchholz shi ne ke rike da kambin duniya na mutumin da aka fi huda ma jiki aka sa ma karafa.

Rolf Buchholz wanda ya so shiga Dubai domin bayyana a wani otel na rawar disco yana da huji daidaidai har guda dari hudu da hamsin da uku a jikinsa da aka masa karafa, da kuma wasu kahonni da aka yi masa guda biyu.

Jami'ai ne a filin jirgin saman Dubai suka hana shi shiga, ya ce sun ce shi matsafi ne.

A yanzu dai Mr Buchholz ya ce har abada ba zai sake kai ziyara Hadaddiyar Daular Larabawan ba.