Hari akan wasu garuruwan Borno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar Boko Haram na kaddamar da hare hare a garuruwan Borno

Rahotanni daga jahar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa wasu da ake zargin cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne sun kai hari tare da kona gidaje a garuruwa akalla biyar dake kan hanyar Dikkwa zuwa Marte.

Wani wanda ya shaida lamarin ya fadawa BBC cewa ya ga gawarwakin mutane da dama akan hanya.

Wannan al'amari ya faru ne da safiyar ranar Lahadi.

Ganau din ya fadawa BBC cewa yaga 'yan bindigar a cikin mota suna kabbara.

Kungiyar Boko Haram ta yi kaurin suna wajen kaiwa garuruwan Borno hari abinda yasa jama'a da dama yanzu haka suka tsere daga gidajensu.