Masu satar bayanai sun yi illa a Rasha

Asusun twitter na Prime Ministan Rasha Hakkin mallakar hoto none
Image caption Asusun twitter na Prime Ministan Rasha

Wata kungiya ta masu satar bayanai a internet, sun yi kutse a asusun twitter na Prime Ministan Rasha a ranar alhamis. Masu satar bayanan sun ari bakinsa suka yi rubutun da suka aika ma kowa cewa "Dmitry Medvedev ya yi murabus."

Shafin na harshen Rasha, wanda ya kunshi mabiya kimanin miliyan biyu da rabi, shi ma an cika shi da rubutun nuna rashin amincewa da Shugaban kasar Vladimir Putin.

Wanda ya yi kutsen ya rubuta cewa Mr Medvedev zai nemi wata sabuwar sana'ar a matsayin dan jarida mai daukar hoto.

Wata kungiyar masu satar bayanai ta Rasha ta yi ikirarin cewa ita ce ta kai ma Prime Ministan da Shugaban kasar wannan hari.

Gwamnati dai a cikin gaggawa ta bayar da tabbacin cewa, an yi kutse a asusun twitter na Prime Ministan.

"Na yi murabus. Matakan da gwamnati ke dauka,sun kunyatar da ni. Ina neman afuwa." Wadannan sune kalaman farko da masu kutsen suka rubuta - daga bisani kuma suka biyo da kamalamai a shafin na twitter cewar za a haramta wutar lantarki, kuma abinda Vladimir Putin ya yi ba daidai ba ne.

Shalty-Bolty - wata kungiya ta masu satar bayanai a shafukkan internet ta ambata cewar ita ce ke da alhakin kai masa harin.

Kungiyar ta kuma yi ikirarin cewa ta yi kutse a asusun Gmail da iPhones na Prime Ministan.

Sakamakon rubuce-rubucen a asusun twitter na Prime Ministan, kungiyar ta kuma yi ikirarin cewa asusun Gmail da rubuce-rubucen da aka yi a wasu wayoyin na iPhone na wasu Prime Ministocin ukku sun fada hannun kungiyar. Daga bisani za a bayar da katin bayani.

To, sai dai ga alama, ba a yi kutsen ba a asusun twitter na harshen Turanci na Mr Medvedev.

Karin bayani