Rikicin Boko Haram ya sa kafa kotun soja

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin da suka zanta da BBC sun ce an sha tura abokansu ana kashewa saboda rashin kayan aiki

Rahotanni sun ce Rundunar sojin Nigeria za ta kafa kotun hukunta sojoji fiye da dari kan zargin nuna ragwantaka da bijire wa umarnin zuwa yaki da 'yan kungiyar Boko Haram a jihar Borno, ko da yake rundunar ta ce matakin ba sabon abu ba ne.

Sojojin sun fito ne daga shiyya ta bakwai ta rundunar sojan Najeriya, kuma bayanai sun nuna cewa an tura su ne zuwa garuruwan Damboa da Gwoza domin su je su aiwatar da aiki

Wasu sojoji da ba su amince a ambaci sunayensu ba, sun shaida wa BBC daga Maiduguri cewa ba da gangan suka bijire wa umarnin manyansu ba, sai dai bisa damuwar da suke da ita ta rashin kayan aiki, kuma ba za su iya tunkarar abokan fafatawarsu, ba tare da isassun kayan aiki ba don gudun halaka.

Sun ce sun san cewa a dokar soja babban laifi ne bijire wa umarnin manya, sai dai a wannan karo sun ce an sha tura abokan aikinsu fagen daga babu isassun kayan aiki, kuma ana hallaka su.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na twitter, mai magana da yawun shalkwatar tsaro ta Nijeriya, Manjo janar Chris Olukolade ya ce ba sabon abu ba ne kafa kotun soja, don hukunta manyan laifuka da suka hadar da nuna ragwantaka, guduwa daga aiki da boren soja