Ebola: Mutane 4 sun warke a Nigeria

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Cutar Ebola ta kashe mutane hudu a Nigeria

Ma'aikatar lafiya ta Najeriya ta ba da tabbacin cewa mutane hudu sun warke daga cutar nan mai kisa ta Ebola, yayinda ake cigaba da killace mutane uku da har yanzu ke jiyyar cutar

Ma'aikatar lafiyar tace, an sallami mutanen ne bayan kwararrun masana kiwon lafiya na ciki da kasashen waje suka tabbatar da cewa sun cika sharuddan da aka tsara na warkewa daga cutar.

Mutanen sun hada da Likitoci maza guda biyu da kuma ma'aikaciyar jinya daya.

Wannan ya sa yanzu haka adadin mutanen da suka kamu da cutar kuma suka warke ya kai mutane biyar

Cutar Ebolan dai ta hallaka mutane hudu a Najeriyar