Hukumar 'yan gudun hijira a Nigeria ta koka

Hakkin mallakar hoto NEMA
Image caption Akwai 'yan gudun hijirar Nijeriya da yawan gaske a jamhuriyar Kamaru

Hukumar kula da 'yan gudun hijira, bakin haure da mutanen da suka rasa matsugunnai a Najeriya ta ce kimanin mutane dubu dari shida ne a jihohin Barno da Adamawa da kuma Yobe a arewacin kasar suka rasa matsugunnansu sakamakon hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram.

Sai dai hukumar ta ce rashin isassun kudi yana kawo nakasu ga yunkurinta na taimaka wa 'yan gudun hijira a kasar.

Yayin wani taron manema labarai a Abuja kan ranar tunawa da masu aikin jin kai ta duniya, Shugabar hukumar, Hajiya Hadiza Sani Kangiwa ta ce suna kokarin ganin an yi gyara ga dokar da ta samar da hukumar don bai wa 'yan gudun hijira taimakon da ya dace a kasar.

Hukumar ta ce akwai 'yan gudun hijira kimanin dubu 50 da suka tsere daga Nijeriya zuwa jamhuriyar Nijar, baya ga wasu dubu 30 da ke samun mafaka a kasar Chadi.