Bincike akan gawar Sarki Richard na III

Hakkin mallakar hoto UNIVERSITY OF LEICESTER
Image caption An hako burbushin kashin kwankwasonsa da na hakarkarinsa da kuma hakoransa

Masu bincike sun debi kashin kwankwaso da kuma hakoran Sarki Richard na III domin gudanar da bincike

Binciken hakoran Sarkin da kuma kasusuwansa sun nuna cewa yana kwankwadar kwalabar barasa guda a rana a shekarun sa na karshe a raye

Binciken wanda jami'ar Leicester ta Burtaniya ta gudanar da kuma wata cibiyar bincike ta kasar, ya nuna irin naman da Sarkin ke ci a lokacin da yake raye

An hako burbushin kashin kwankwasonsa da na hakarkarinsa da kuma hakoransa a Leicester a shekarar 2012

Binciken ya gano cewa abincin da yake ci mai rai da lafiya ne fiye da wadanda sauran mutane masu irin matsayinsa suke ci a wancan lokacin

Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Binciken ya nuna cewa yana cin abinci mai rai da lafiya a lokacin da yake raye

Daya daga cikin masu binciken Angela Lamb daga jami'ar Leicester ta ce 'mun fahimci cewa yana liyafa sosai, an kuma gano barasa cikin liyafarsa kuma da alama hakan ya yi tasiri a jikinsa a 'yan shekarunsa na karshe a raye

Takardar da aka rubuta rahotan binciken tace binciken da aka yi akan kasusuwansa da hakora ya nuna dabi'arsa ta shaye shaye ta canza matuka a lokacin da ya zama Sarki a shekarar 1483

Binciken ya kuma nuna cewa Sarkin ya fice daga gabashin Ingila yana da shekaru bakwai, inda ya koma zama a yammacin Ingilan maiyiwuwa a Weslh Marches

Sarki Richard na III, wanda ya yi mulki daga shekarar 1483, an kashe shine a yakin Bosworth a watan Agustar shekarar 1485

Amma kabarinsa ya bace a lokacin da aka rushe cocin dake harabar inda aka binne shi