Jiragen Yaki na shawagi a Tripoli

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Ba a san inda wadannan jiragen yaki suka fito ba

Mazauna birnin Tripoli babban birnin Libya sun ce wasu jiragen yaki da ba a san inda suka fito ba, suna shawagi a sararin samaniyar birnin.

An kuma ji karar fashewar bama-bamai da dama.

Wani wani wakilin BBC a Tripoli ya ce, wani babban jami'i na ma'aikatar harkokin wajen kasar ya nuna cewar gwamnati ba ta da masaniyar ko daga inda jiragen yakin suka fito.

Bayan wasu rahotanni na kafofin watsa labarai na kasar sun zargi Faransa da Italiya da kungiyar tsaro ta NATO, wani jami'in Majalisar dinkin duniya a Tripoli ya shaidawa wakilin BBC cewar, babu hannun daya daga cikin wadanda ake zargi.

Babu dai daya daga cikin kungiyoyin dake gaba da juna da ta yi ikirarin kai harin ta sama.