Wani matashi ya tallata kansa neman aiki

Tashar jirgin kasa na waterloo a London Hakkin mallakar hoto
Image caption Tashar jirgin kasa na waterloo a London

Alfred Ajani daya ne daga cikin dubban daliban da suka kammala karatunsu na degree a baya bayan nan wadanda ke ta fadi tashin neman aiki.

Ya aika takardar neman aiki a wurare kimanin 300 amma bai yi nasara ba.

A karshe ya yanke shawarar tsayawa a tashar jirgin kasa na Waterloo a London lokacin da jama'a suke kai komo yana mika musu takardar bayanin karatunsa da kuma kwarewar da ya samu.

Matakin da ya dauka ya sami tagomashi inda cikin 'yan sa'oi ya rika samun waya mai karfafa gwiwa.

A yanzu dai yana fatan cimma burinsa na samun aiki bayan samun gayyatar ganawa ta daukar aiki wato Interview.

Karin bayani