Manyan motoci masu tuka kansu

Hakkin mallakar hoto AP

Rahotanni sun ce za a iya gwajin manyan motoci masu dakwon kaya dake tuka kansu akan titunan Burtaniya nan zuwa shekara mai zuwa.

Fasaha ce ta bada damar ayarin manyan motocin daukar kayan su yi jerin gwano suna tafiya, tare da direba kwaya daya a gaba wanda zai jagorance su.

Wannan sabuwar fasaha da aka kirkiro zata taimaka wajen rage yawan man fetur da ake sha, in ji wadanda ke goyan bayan shirin.

Sai dai wasu kungiyoyi sun soki shirin wanda suka ce zai rika tsoratar da sauran mutanen dake kan titi.

Jaridar Sunday Times ta ruwaito cewa ministocin Burtaniya sun ziyarci Kasar Sweden domin ganewa idonsu yadda wannan sabuwar fasaha take a aikace

Za kuma ayi gwajin fasahar a badi a Burtaniya.

Sai dai a wata sanarwa da ya fitar, sashen kula da harkokin sufuri ya ce 'Ba a yanke shawara ba akan gwajin sabuwar fasahar'

'Kuma tsaron titi shine abu mafi mahimmanci da ba zamu yi wasa da shi ba'

Sabuwar fasahar ta bukaci a sami direba a cikin kowacce babbar mota saboda idan ta-baci.

Amma mafiyawanci direbobin zasu sakata ne kawai su wala, imma su kasance suna karatun littafi ko kuma cin abinci kamar yadda aka tsara

Wani direba ne dake gaba zai jagoranci ayarin manyan motocin inda kowacce babbar motar zata rinka bada bayanai ta hanyar kafar sadarwa ta wi-fi.

Za kuma ayi amfani da kamarori da wasu na'urori domin sanin duk inda motar ta motsa

Kamfanoni da dama na gudanar da bincike game da irin wannan fasaha da suka hada da kamfanin Marsidis- Benz