Ebola: Babbar Likita ta mutu a Najeriya

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Mutane biyar ne suka mutu ke nan yanzu a Nigeria

Wata sanarwa data fito daga ma'aikatar lafiya a Najeriya na cewa wata kwararriyar Likita ta rasu sakamakon kamuwa da cutar Ebola.

Dr. Ameyoh Adadevoh ita ce ta jagoranci likitocin da suka duba lafiyar dan Liberiyan nan marigayi Patrick Sawyer.

Ma'aikatar lafiyar ta ce mutane biyar ne ke nan yanzu haka suka mutu a Najeriya sakamakon kamuwa da cutar.

A ranar Litinin ne dai ma'aikatar lafiyar Najeriyar ta bayyana cewa wasu mutane 4 sun warke daga cutar Ebolan.

Mutuwar Dr. Adadevoh na zuwa ne daidai lokacin da hukumar lafiya ta duniya WHO ke yabawa matakan da Nigeria take dauka wajen hana yaduwar cutar