WHO: Ana samun nasara a yaki da Ebola

Image caption Hukumar ta ce tsananin bincike da kokarin bibiyar cutar ya sa kyakkyawan fatan dakatar da ita

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce alamu na nuna cewa ana ci gaba da samun nasara a kokarin dakatar da yaduwar cutar Ebola a kasashen Najeriya da Guinea.

Hukumar ta ce yanayin da ake ciki a Lagos, inda cutar ta bulla a Nijeriya yana da karfafa gwiwa don kuwa mutane 12 da suka kamu da cutar, sun samo tushe ne daga Patrick Sawyer.

Ta ce karuwar mutanen da ke warkewa daga Ebola a Nijeriya ya nuna cewa hakika ana iya warkewa daga wannan cuta.

Haka zalika, binciken da Hukumar lafiya ta Nijeriya da hadin gwiwar cibiyar kula da cutuka masu yaduwa ta Amurka ya nuna cewa babu wani Dan Nijeriya da ya kamu da cutar ba ta hanyar Dan Laberiya Patrick Sawyer ba.

Haka kuma, cutar Ebola a Guinea, inda ta fara bayyana bara a yankin Afirka ta yamma, ba ta tayar da hankali kamar a kasashen Laberiya da Saliyo