Ebola: An gano mutanen da suka bace

Yaki da Ebola a Liberia
Image caption Yaki da Ebola a Liberia

Gwamnatin Laberiya ta ce ya zuwa yanzu ta gano dukkanin mutane 17 da ake zargin suna dauke da cutar Ebola amma suka kubuce bayan hari da aka kai wata Cibiya da aka killace su a karshen mako.

Ministan yada labaran Kasar Lewis Brown ya fada wa BBC cewa an kai mutanen zuwa wata cibiyar lafiya ta kwararru.

An dai tsaurara tsaro a cibiyoyin killace masu Ebola bayan an kai wa cibiyar hari lamarin da ya sanya fargabar cewa cutar ka iya ci gaba da yaduwa a kasar.

Alkaluman Hukumar lafiya ta duniya na baya-bayan nan sun ce kimanin mutane 1,229 ne ya zuwa yanzu suka mutu sakamakon cutar Ebola, kuma mafi yawancinsu daga Laberiya.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce tana kokarin shirya kai agajin abinci ga mutanen da ke

Karin bayani