An yi bore kan hana zirga-zirga a Liberiya

Hakkin mallakar hoto
Image caption A karshen makon jiya ne wasu mutane suka auka wa wata cibiyar masu Ebola kuma suka washe ta a yanki

'Yan sanda a Laberiya sun harba hayaki mai sa hawaye don tarwatsa cincirindon wasu mutane masu zanga-zanga a kan kakaba wa unguwarsu da ke Monrovia babban birnin kasar, dokar killacewa.

Shaidu sun ce mazauna yankin a fusace na jifa da duwatsu kan jami'an tsaro da aka jibge don tabbatar da hanin gwamnati na zirga-zirga.

Unguwar dai tana cikin yankin da aka kai hari tare da washe wata cibiyar masu Ebola a karshen mako, lokacin da majinyata 17 da ake zaton suna dauke da cutar Ebola suka bata amma daga bisani aka gano su.

Shugaba Ellen Johnson Sirleaf ta ba da umarnin hana zirga-zirgar dare don takaita yaduwar cutar Ebola a fadin kasar.

Yanzu dai adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar Ebola ya karu zuwa fiye da 1,200