MSF ta soki Hukumar lafiya a kan Ebola

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Cutar ta barke ne a kasashen Guinea, Saliyo da Liberiya da kuma Nijeriya a baya-bayan nan

Kungiyar Likitoci ta Médecins Sans Frontières ta soki lamirin matakin Majalisar Dinkin Duniya da hukumar lafiya ta duniya suka dauka kan cutar Ebola a yankin Afirka ta yamma.

Daraktan aikace-aikace na kungiyar, Brice de La Vigne ya kwatanta matakin da hukumomin suka dauka sakamakon yaduwar cutar ta Ebola da cewa bai taka kara ya karya ba.

Ya ce kusan an bar kungiyarsa da dawainiyar tunkarar barkewar cutar ita kadai a yankin.

Gwamnatoci a Afirka ta yamma na fafutukar dakile yaduwar Ebola da ya zuwa yanzu ta hallaka mutane fiye da 1,200 tun bayan barkewarta a watan Maris.