Isra'ila ta kuskure wani kusan Hamas a Gaza

hare hare a Gaza Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption hare hare a Gaza

Mayakan Hamas sun ce jagoran rundunar sojinsu Mohammed Deif ya tsira daga yunkurin hallaka shi da Isra'ila ta yi.

Isra'ilar ta ce ta yi niyyar kai wa Mr Deif hari ta sama a Gaza ranar Talata ne inda kuma matarsa da jaririnta suka hallaka.

Dubannin masu jimami ne suka yi tururuwa kan titunan Gaza don yin jana'iazarsu, suna mai rerewa taken daukar fansa.

Mayakan Hamas din dai sun harba rokoki kusan 60 kan Isra'ila, yayinda Isra'ilar ta kaddamar da hari ta sama kusan sau dari kan Gazar.

Palasdinawa sun ce akalla mutane 20 suka hallaka a sabon fadan da ya barke.