An kera motar google maras matuki

Kananan motocin google masu tuka kan su da kan su Hakkin mallakar hoto Google
Image caption Kananan motocin google masu tuka kan su da kan su

An kera Kananan motoci na Google kuma an shirya su, su zarce gudun da aka kayyade da kilomita 16 cikin sa'a guda, kamar yadda Injiniyan kere-kere na motocin kamfanin ya bayyana.

Dmitri Dolgov ya gaya ma kamfanin dillancin labarai na Reuters cewar a yayinda motocin dake kusa da motar ke karya doka ta kayyade gudu, tafiya sannu a hankali za ta iya haddasa hadari, don haka motar ta Google ke kara mai don jerawa da su.

An yi gwajin samfurin Motar mai tuka kan ta da kan ta, ta Google a kan hanyoyi a Amurka.

Daga shekara ta 2015, Brittaniya za ta ba da dama a rinka amfani da motocin maras sa matuka a kan hanyoyin da sauran motoci ke amfani da su.

A shekara ta 2010 ne kamfanin na Google ya fara ba da sanarwar sashen sa na kera motoci maras matuka, kuma tun lokacin yake gwajin fasahar a wasu kananan motoci da aka canza ma fasali wadanda wasu kamfanoni suka kera.

Motocin sun yi tafiya ta fiye da mil 300,000 a kan hanya yawanci a California.

A watan Mayu, kamfanin fasahar na Amurka ya ambata cewar zai fara kera kananan motocinsa masu tuka kansu da kan su.

Motocin masu siffar kubba suna wurin zaman mutum biyu, wutar lantarki ce za ta rinka tafiyar da su, kuma tashin farko za a kayyade gudun su ne zuwa kilomita 40 a sa'a guda don taimakawa a tabbatar da tsaron lafiya.

A watan Yuli, gwamnatin Brittaniyya ta sanar da cewa daga watan Janairu na badi, za a bar motoci masu tuka kan su su rinka tafiya a kan hanyoyin da sauran motoci ke amfani da su.

Bugu da kari, Ministoci sun ba da umurnin a sake nazarin dokokin hanya na Brittaniya don samar da dokokin da suka cancanta.

Karin bayani