Ebola: Dokar hana zirga zirga a Liberia

Wasu 'yan kasar a Monrovia Hakkin mallakar hoto
Image caption Mazauna Liberia na watsi da shawarar jami'an lafiya akan cutar Ebola

Gwamnatin Liberia ta kafa dokar hana yawace-yawace tare da killace wani bangare na Monrovia babban birnin kasar a yayinda take gwagwarmayar shawo kan bazuwar cutar Ebola.

Shugaba Ellen Johnson Sirleaf ce ta bayar ta sanarwar hana zirga-zirga a ciki da wajen yankin yammacin birnin.

Yankin dai shine aka kai ma hari a kan wata cibiyar kiwon lafiya a karshen makon da ya wuce lokacinda majiyyata cutar ta Ebola 17 suka bace.

Kamfanin sufurin jiragen sama na kasar Kenya ya dakatar da sauka kasar ta Liberia da makwabciyar ta Saliyo.

Adadin mutanen da suka mutu sakamakon cutar ta Ebola a yammacin Afrika ya zarce dubu da dari biyu.