Gobara ta lakume Shalkwatar NFF

Image caption Fifa ta dakatar da Nijeriya ne saboda ta nada wani jami'i don ya jagoranci Hukumar a watan jiya

Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya da ke fama da rikicin cikin gida ta sake tsunduma cikin wani hali sakamakon tashin gobara a shalkwatarta.

Gobarar ta tashi ne lokacin da Ma'aikata suka fara zuwa aiki daga wani ofishi, inda kuma nan take ta bazu zuwa sauran sassan ginin, kafin isar ma'aikatan kashe gobara su murkushe ta.

Wani darakta a Hukumar, Emmanuel Ikpeme ya ce ga alama gobarar ta tashi ne a ofishin wani babban akanta, inda ta bazu zuwa ofishin babban sakataren Hukumar.

Hukumar na fama da rikicin shugabanci tsawon watanni, lamarin da ya sa Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta dakatar da Nijeriya a watan jiya kan abin da ta kira "katsalandan din gwamnati" cikin harkokin kwallon kafa, amma daga baya ta dage dakatarwar.