Mayakan ISIS 'sun yanke kan dan jarida'

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Foley ya bace daga Syria shekaru biyu da suka gabata

Amurka ta ce tana kokarin tantance sahihancin wani hoton bidiyo wanda ya nuna mayaka na kungiyar ISIS suna datse kan wani dan jarida na Amurka James Foley

Mr. Foley ya bace daga Syria kimanin shekaru biyu da suka gabata kuma tun lokacin ba a ji duriyarsa ba.

Mahaifiyar Mr. Foley din Diane ta aike da sakon juyayi ga dan na ta, ta hanyar sadarwa ta Facebook, tana cewar ya rasa ransa ne a yayinda yake kokarin bayyana halin kunci da mutanen Syria suka shiga.

Ta kuma yi kira ga wadanda suka sace shi, su ceci rayukan sauran mutanen da suke garkuwar da su.

Ta bayyana cewar, ba su aikata laifin komai ba, kuma ba su da iko a kan manufar kasashen waje ta Amurka.