Afirka ta Kudiri yaki da Ebola

Taron shugabannin Afirka
Image caption Taron shugabannin Afirka

Kungiyar Tarayyar Afirka za ta tura wani ayari na musamman zuwa kasashen Afirka hudu da ke fama da annobar cutar Ebola.

Kwamitin Sulhu na Kungiyar ya ce wannan aiki da ayarin zai yi zai ci dala miliyon ashirin da biyar, kuma za su yi aiki ne tara da hadin-gwiwar Amurka da wasu.

Kwsamishina mai lura da walwala da jin dadin jama'a a kungiyar ta tarayyar Afirka Dr Mustapha Sidiki yace tawagar za ta kunshi dakarun soji da kuma jami'ai na farar hula da likitoci masu aikin sa kai da jami'n jinya da kuma sauran ma'aikatan asibiti.

A karshen wannan watan na Augusta ne tawagar za ta fara aiki wanda kuma ake sa ran za su dauki tsawon watanni shida suna yi.

Tun farko a wannan watan kungiyar tarayyar Afirkar ta ce za ta bayar da dala miliyan daya daga asusunta na taimakon jin kai domin tallafawa yunkurin da ake kan yi na shawo kan annobar cutar a kasashen Guinea da Saliyo da Liberia da kuma Najeriya.

Karin bayani