'Boko Haram ta kwace Buni Yadi'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau

Rahotanni sun nuna cewa kungiyar Boko Haram ta kwace iko da garin Buni Yadi na jihar Yobe da ke arewacin Nigeria.

Garin Buni Yadi shi ne na baya-bayan nan da ya fada hannun kungiyar Boko Haram wadda bisa dukkan alamu take kara karfi a yankunan da ke jihohin Borno da Yobe.

Mazauna garin sun shaida wa BBC cewa mutane da dama sun tsere daga Buni Yadi saboda rashin jami'an tsaro.

Kakakin gwamnan jihar Yobe, Abdullahi Bego ya ce "Babu sojoji a Buni Yadi kuma mazauna garin sun ce 'yan Boko Haram suna shiga garin suna fita a duk lokacin da suke so."

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da rahotanni ke cewa kungiyar Boko Haram ta karbe iko da wata makarantar horar da 'yan sanda da ke Limankara a Gwoza.

Bayanai sun nuna cewa a makonnin da suka wuce 'yan Boko Haram sun kwace garuruwan Damboa da Gwoza a jihar Borno.

Ko da yake wasu rahotanni sun ce sojojin Nigeria sun kara kwace garin Damboa a cikin farkon wannan watan.