An gaza kafa gwamnati a Afirka ta Tsakiya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sabon Firaministan, Mahamat Kamoun da Shugabar riko Catherine Samba Panza

Kwanaki goma sha daya kenan ya zuwa ranar laraba, babu gwamnati a Jamhuriyar tsakiyar Afrika.

Sabon Firai Ministan kasar, Mahamat Kamoun har yanzu ya kasa samun karbuwa a wajen tsoffin 'yan tawayen Seleka da wasu kungiyoyin siyasa.

Lamarin da ya sa aka kasa cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa a kasar.

Hakan kuma ya sake haifar da rigingimu, don kuwa yunkurin raba kasar gida biyu ne ya fi samun karbuwa a tsakanin wani bangare na tsoffin 'yan tawayen seleka.

A daya bangaren kuma, ana ci gaba da gwabza fada tsakanin masu rike da makamai da kuma dakarun Faransa.

Karin bayani