Likitan da ya kamu da Ebola ya warke

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fiye da mutane 1,000 ne suka rasa rayukansu sanadiyyar cutar Ebola a Afrika ta Yamma

Likitan nan Ba amurke da ya kamu da cutar Ebola a Liberia ya warke kuma an sallame shi daga asibiti a Amurka.

An bai wa Dr. Kent Brantly maganin Zmapp da ake gwajin shi a lokacin da ake kula a wani asibiti da ke jihar Atlanta ta Amurka.

Hakan na zuwa ne yayin da wasu likitoci uku da suka kamu da cutar a Liberiya ke ci gaba da samun sauki, bayan an ba su maganin na Zmapp.

Sai dai kamfanin da ya hada maganin ya ce a yanzu babu sauran maganin da ya rage.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba