Kwayoyi: Obasanjo ya kalubalanci shugabanni

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dumbin kudaden da ake samu a harkar miyagun kwayoyi yasa dillanta ka iya sayen jami'an tsaro

Shugaban Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma, Cif Olusegun Obasanjo ya kalubalanci kasashen yankin kan yaki da miyagun kwayoyi.

A ranar Laraba ne Cif Obasanjo ya mika rahoton da hukumar ta fitar ga shugaban ECOWAS kuma shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama.

A rahoton da hukumar ta fitar a watan Yunin da ya wuce, hukumar ta nemi gwamnatocin Afrika ta yamma su sassauta dokokin yaki da ta'ammali da kwayoyi, su kuma yi wa lamarin duban wata matsala ta lafiya.

Tsohon shugaban Najeriyan ya ce miyagun kwayoyi na yin zagon kasa ga kwanciyar hankali da ci gaban kasashen Afirka ta yamma, kuma ba kawai birkita rayuwar matasa suke yi ba, har ma suna nakasa tsarin siyasa da shari'a da kuma shugabancin yankin.

Bayanai na nuna cewa an dade ana noma da kuma shan tabar wiwi a Afrika ta Yamma, sai dai a tsawon shekaru raunin shugabanci a kasashen yankin ya sanya yankin zama wani babban zango na hodar iblis daga kasashen Latin Amurka zuwa nahiyar Turai.