'Garin Gwoza ya koma daular Musulunci'

Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban kungiyar Boko Haram a Nigeria Abubakar Shekau, ya yi ikirarin cewa, garin Gwoza da suka kwace daga hannun dakarun Najeriya, a yanzu ba ya karkashin Najeriyar, ya koma karkashin daular musulunci.

Abubakar Shekau ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo na mintuna 52 da kamfanin dillancin labarai na AFP ya samu.

Sai dai abinda bai fito fili ba shi ne, ko yana nufin daular Musulunci karkashin Jagorancin Abubakar Al Baghdadi ta Iraq ko kuma wata daular Musuluncin ta daban suka kafa a Nigeria.

Sai dai a martanin da ta mayar ga sakon bidiyon, shalwatar tsaron Najeriya ta karyata ikirarin da kungiyar Boko Haram ta yi na cewa ta mayar da garin Gwoza da ke cikin jihar Borno a yankin Arewa masu Gabashin Najeriya a karkashin daular musulumci.

A wata sanarwa da kakakin shalkwatar tsaron Najeriya Manjo Janar Chris Olukolade ya wallafa a shafin sada zumunta na twitter ya ce, wannan ikirari na shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ba shi da tushe balle makama.

Olukolade ya kuma kara da cewa, 'yanci da daukacin farfajiyar Najeriya na nan yadda ya ke, kuma ba za a amince da duk wani ikirari na wata kungiyar ta'adanci da ke cewa ta mamaye wani bangare na kasar ba.

Sanarwar ta kuma ce a yanzu haka sojoji na ci gaba da gudanar da ayyuka na kwato yankin daga hannun wadanda ta kira 'yan bindiga.

Hoton bidiyon na Boko Haram dai ya nuna wasu mutane kwankwance inda aka bindige su, da kuma wasu mutane biyu da aka ce sun sanya kayan mata don su samu tsere wa, su ma aka harbe su.

Karin bayani