'Ba a yi wa 'yan matan Indiya biyu fyade ba'

Image caption Wasu rahotanni sun ce za a saki wadanda ake tsare da su muddin ba a gurfanar da su ba nan da 'yan kwanaki

Rahoton wani binciken da aka gudanar a kan gawawwakin 'yan matan nan biyu da aka samu a rataye a kan bishiya a Indiya ya nuna cewa ba a yi musu fyade ba.

Hakan dai ya sha bambam da sakamakon gwajin farko da aka yi kan gawawwakin 'yan matan biyu da aka kashe a watan Mayun da ya wuce.

'Yan sanda a yanzu na kallon lamarin kisan 'yan uwan biyu masu shekaru 14 da 15 ta fuskar "Kisan Martabawa".

Ana rike da wasu mutane uku da kuma wasu 'yan sanda biyu da ake zargi da hannu a al'amarin.