Amurka ta yi kokarin kubatar da Foley

Iyayen James Foley Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Iyayen James Foley

Hedikwatar tsaron Amurka, ta ce sojojin kasar na musanman sun yi kokarin kubutar da wasu Amurkawa da aka yi garkuwa da su a Syria a farkon wannan shekarar, da suka hada da James Foley.

Shi ne dan jaridar da mayakan kungiyar da ke da'awar kafa daular musulunci suka halaka, kisan da ya jawo suka daga kasashen duniya.

Jami'an ma'aikatar tsaron Amurka suka ce aikin kokarin kubutar da Amurkawan wanda akayi cikin sirri, shi ne na farko da sojin Amurkan suka yi a Syria.

Jami'an sun kara da cewa, an sako zaratan sojojin Amurka na musanman ta jiragen sama a wani yanki da ke hannun mayakan kungiyar 'yan gwagwarmayar.

Sojojin sunyi musayar wuta da mayakan kungiyar amma ba su yi nasarar gano ko da daya daga cikin Amurkawan ba, haka kuma suka kammala aikin ba tare da nasara ba, in ji jami'an.