An gano hanyar satar shiga Gmail

Manhajar Amazon ce ta dan yi wuyar shiga, amma an yi nasarar kutsawa cikinta da kashi 48 cikin dari.

Asalin hoton, Getty

Bayanan hoto,

Manhajar Amazon ce ta dan yi wuyar shiga, amma an yi nasarar kutsawa cikinta da kashi 48 cikin dari.

Masu bincike a Amurka sun ce sun samu nasarar kutsawa cikin akwatunan wasikun mutane na Gmail, saboda raunin tsaro na wasu manyan wayoyin salula.

Masu binciken suka ce sun samu nasarar kutsen ne cikin manhajoji da yawa na wayoyin, da suka hada da ta Gmail, ta hanyar amfani da wata manhaja ta bogi da ke yaudarar masu wayar salula a matsayin wadda za ta kara inganta aikin wayoyinsu.

Binciken ya nuna cewa manhajar aikawa da sakonni ta Gmail na daga cikin wadanda ake iya kutsawa cikinsu a saci bayanai ba tare da an sha wahala ba.

Wata mai magana da yawun kamfanin babbar manhajar Google ta ce sun yi maraba da wannan bincike.

Ta ce ''irin wannan bincike da wasu daban suke yi yana daya daga cikin abubuwan da suka daukaka babbar manhajar Android, kuma suka sa take da tsaro.''

Masu binciken daga jami'o'in Michigan da California za su gabatar da sakamakon binciken nan gaba a wurin wani taro kan tsaron aikace-aikace ta intanet a San Diego.

Sauran manhajoji da aka iya kutsawa cikinsu don nadar bayanai sun hada da manhajar H&R Block wadda ake biyan haraji da ita, da Newegg wadda ake iya siyayya ta intanet da ita, da WebMd, da Chase Bank, da Hotels.com da Amazon.

Binciken ya nuna cewa manhajar Amazon ce ta dan yi wuyar shiga, amma dai an samu nasarar kutsawa cikin ta da kashi 48 cikin dari.

Kutsen ya hada da shiga runbun adana bayanan aikin kowacce manhaja a cikin wayar salula, ta hanyar yin amfani da barauniyar manhajar satar bayanai, wadda ta ke zuwa wa masu amfani da waya ko dai a matsayin abin da zai ba wayoyinsu kariya, ko kuma hoto na kawata fuskar wayoyin.

Masu binciken suka ce kowacce manhaja a cikin waya tana amfani da runbun, kuma ta haka, za a iya gane lokacin da mutun ya ke shiga cikin akwatin aika sakonninshi na Gmail, wanda ke ba da damar a satar mi shi bayanan sirri da yake amfani da su wajen shiga cikin akwatin.

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Binciken ya gano hatta bayanan banki na ajiya za a iya sata

Daya daga cikin masu binciken, Zhiyun Qian na jami'ar California ya ce mutane suna daukar cewa aikin wata manhaja a cikin waya bai shafi na wata ba.

''Yanzu mun nuna hakan ba gaskiya ba ne.

Manhaja daya tana iya tasiri babba akan wata, kuma hakan ka iya haifar da babbar illa ga mutun.''

Masu binciken sun kuma gano cewa za a iya satar hotuna da ake dauka idan mutane za su yi siyayya ta intanet ta yin amfani da manhajar Chase Bank, wanda hakan ke ba da damar satar bayanan banki da mutane ke amfani da su.

An gwada kutsawa cikin manhajojin ne akan wayoyi masu amfani da manhajar Android, amma masu binciken suka ce suna da yakinin za a iya kutsawa a nadi bayanai daga wayoyin da ke amfani da manhajojin Windows da IOS na kamfanin Apple.