An kashe masallata da yawa a Iraki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An kashe mutane da dama a cikin masallaci a Iraki

Jami'an tsaro a Iraki sun ce mutane da yawa ne aka kashe a wani hari a kan wani masallacin 'yan Sunni a lardin Diyala na gabashin kasar.

Rahotanni sun ce wani dan kunar bakin wake ne ya tayar da bam a cikin masallacin a lokacin sallar Juma'a, sannan wani dan bindiga ya bude wuta a kan masallata da ke tserewa.

Wasu kafofin watsa labaran Iraki sun zargi sojin sa kai na 'yan Shi'a game da harin, to amma wasu rahotannin sun ce ramuwar gayya ce daga kungiyar masu jihadi ta 'yan sunni ta kasar musulunci, bayan da ta rasa iko da yankin.

Yankin dai ya yi fama da matsanancin fada a yan makunnin nan.

Karin bayani