Turkman a Iraki suna fuskantar barazana

Al'ummar Turkman na Iraki Hakkin mallakar hoto AFP

Jami'an Majalisar Dinkin Duniya a Iraki suna gargadi game da yiwuwar kashe kashen rayukan jama'a a wani gari inda mayakan kasar musulunci suka yi wa dubban yan Shi'a 'yan al'ummar Turkman marasa rinjaye kawanya.

Jakadan musamman na Majalisar Dinkin Duniya a Iraki ya ce mazauna yankin su kimanin dubu goma sha takwas suna fuskantar matsannacin hali da ba zai misaltu ba a garin Amerli wanda aka katse daga samun abinci da ruwan sha kusan watanni biyu ke nan.

Halin da dubban mutanen da mayakan Daular Islama suka yi wa kawanya a garin Amerli mai tsanani bisa dukkan rahotanni, inda ba su da isasshen abinci, ko ruwa ko kuma magunguna.

Agaji kadan ne sojin Iraki suka kai ta helikwabtoci, kuma kadan ne daga cikin wadanda suka sami raunuka aka sami fitarwa.

Sai dai bayan tsananin da suke ciki, akwai kuma tsoron abin da ka biyo baya.

Tsirarun da ke bin wasu addinai da dakarun na Daular Islama suka kama suna yin sa'a ne idan suka sami tsira da rayukansu, kuma da yawa, musamman daga cikin mabiya addinin Yazidi a Sinjar, an kashe su.

Mataimakin wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman Iraki, Gorgy Busztin, ya fito karara ya bayyana damuwa.

Ya ce, "Muna tsoron irin abin da ya faru a Sinjar, da Tell Afar, da Tell Keif, inda dakarun ISIS suka darkake mutanen da kin wata akida ta Islama da ba tasu ba.

"Mun damu cewa abin da ya auku a baya zai iya sake aukuwa."

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga gwamnatin Iraki da sauran kasashen duniya da su dauki matakin gaggawa don kauce wa kisan kare dangi.