Motocin agaji na Rasha sun koma gida

motocin agaji na Rasha Hakkin mallakar hoto AP

Manyan motoci da suka kai kayan agaji zuwa Yukuren daga Rasha a yanzu sun koma Rashar, bayan da suka kai kayan agajin zuwa birnin Luhansk da ke hannun 'yan tawaye ba tare da sun sami izinin shiga Yukuren din ba daga hannun gwamnatin kasar.

An dai ta kace-na-ce tsawon kwanaki a kan ayarin motocin su fiye da dari biyu.

Sun bar Ukraine din ne a dai lokacin da Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta isa Kiev, babban birnin Yukuren din domin tattaunawa.

Da ma dai Rasha ta nace ne a kan cewa ayarin motocin na agaji ne kawai...wanda ake nufin kaiwa birnin na Luhansk da ke hannun 'yan tawaye, wanda sojin gwamnatin Yukuren suka yi wa kawanya...aka kuma yanke masa wuta da ruwa.

Sai dai tun farkon tafiyar ayarin agajin an yi ta zarge-zarge a kan abin da ke cikin wadannan motoci...da kuma tunanin watakila batun kai agajin wani alaye ne na agaza wa 'yan tawayen da al'amurra suka soma kwance masu...ko kuma kamar Yukuren ke cewa, watakila share fage ne na kawo hari daga Russia.

Bayan kai-kawon da akai ta faman yi game da bincika abin da ke cikin motocin, jiya dai ayarin ya shiga Ukraine ba tare da iznin gwamnatin kasar ba.

Kasashen Yammacin duniya sun bi sahun Yukuren wajen yin Allah wadai da shigar a matsayin abin da ya saba wa doka, tare da neman ayarin ya fita.

Dazun Kungiyar Tsaro da Hadin Kai ta Turai ta tabbatar da komawar motocin zuwa Rasha.

Wani kakakin gwamnatin Yukuren ya yi zargin cewa yayin da motocin Rashar ke cikin Yukuren an cika su ne da kayayyaki daga cibiyoyin sojin kasar ta Yukuren.

Bayan da ta gana da Shugaban Ukraine din, Petro Poroshenko a birnin Kiev, Shugabar Jamus, Angela Merkel, ta ce ba za a sami dawwamammen zaman lafiya ba, har sai an sami yarjejeniya ta kwarai game da yadda za a dinga sa ido sosai a kan iyakar Yukuren din da Rashar.