An sace kayan mata masu yi wa coci hidima

Image caption Hukumar SSS ta ce mutanen da suka saci kayan Rabaran Sistas za su iya shammatan jama'a su aikata ta'addanci

Hukumar tsaro ta farin kaya SSS a Najeriya ta ce wasu mutane da ba a san ko suwaye ba, sun balle shagon wani tela a unguwar Sabon Gari da ke jihar Kano a arewacin kasar, inda suka sace wasu kayan mata masu yiwa coci hidima 13.

Mataimakiyar daraktan yada labarai na hukumar, Marilyn Ogar cikin wata sanarwa ta ce satar kayan ta kara fargabar yiwuwar yin amfani da su wajen kaddamar da ayyukan ta'adanci a kasar.

Hukamar ta ce akwai bukatar jama'a su sa ido sosai ga mutane masu sanye da irin wadannan kaya na mata masu yiwa cocin Katolika hidima da ake kira Rabaran Sistas, don kaucewa abinda ya faru a baya, inda aka yi amfani da wasu mata sanye da hijabi wajen kai hare-haren kunar bakin wake.

Ta kuma bukaci jama'ar kasar da su rika taimakawa hukumomin tsaro da bayanai akan mutanen da basu gane take-taken su ba.