Boko Haram ta bayyana kafa Daular Musulunci

Boko Haram

Shugaban kungiyar Boko Harama a Najeriya Abubakar Shekau, ya ya yi ikirarin cewa, garin Gwoza da suka kwace daga hannun dakarun Najeriya, a yanzu ba ya karkashin Najeriya, ya koma karkashin daular musulunci.

Abubakar Shekau ya bayyana hakan ne a cikin wani faifan bidiyo mai mintuna hamsin da biyu da kamfanin dillancin labarai na AFP ya samu.

Gwamnatin Najeriya dai ta ce sanarwar ta Boko Haram shirme ce, kuma Najeriya tana nan a matsayin kasa guda.

Kana sojin Najeriyar suna nan suna kokarin kwato duk wasu yankuna da ke hannun kungiyar ta Boko Haram.

Sai dai kungiyar ta Boko Haram tana rike da wasu yankunan na jihar Borno ta Najeriyar tsawon lokaci.

Sannan har yanzu hukumomin Najeriyar ba su kwato ‘yan matan Chibok da wasu matan da kungiyar ta Boko Haram ta sha kamawa ba.