Digirin digirgir a Cakulan

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Cakuleti na narkewa a yanayi na zafi

Za a bai wa masana kimiyya da kuma ma'abota shan Cakulan damar yin digirin digirgir a kan Cakulan a jami'ar Cambridge da ke Ingila.

Kalubalen shi ne a hana Cakulan daga narkewa a yanayi na zafi.

Za kuma a yi haka ne ta hanyar nazarin abubuwan da ake bukata kada alawar ta narke a yanayin zafin.

Za a bai wa masu sha'awar neman wannan dama zuwa ranar 29 ga watan Agusta domin su cike takardunsu na nema.

Ana tsammanin duk wanda ke da sha'awar yin digirin digirgir a kan Cakulan ya gudanar da bincike a kan abubuwan da za su sa alawar ta kasance yadda take a dunkule, ba tare da ta narke ba idan aka ajiye ta da kuma sayar da ita a yanayi mai zafi.