Tattalin arziki: An rusa gwamnati a Faransa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sakon da shugaba Hollande ke aike wa shi ne ba zai lamunci wadanda suka juya masa baya ba

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande, ya sanar da rushe gwamnatinsa bayan sukar lamirin manufofin tattalin arzikinta a bainar jama'a da wasu Ministoci biyu suka yi.

Mr. Hollande ya bukaci Firai minista, Manuel Valls ya kafa wata sabuwar gwamnati nan da ranar Talata.

Hakan dai ya biyo bayan kiran da ministan tattalin arziki, Arnaud Montebourg da kuma ministan ilimi suka yi kan Faransar ta sauya shirinta na tsuke bakin aljihun gwamnati domin cike gibin da rage kudaden haraji ga 'yan kasuwa zai jawo.

A karshen mako ne dai ministan tattalin arzikin ya ce tsuke aljihun gwamnati na dakushe ci gaban kasa, kuma a bayyane yake cewa ana samun durkushewar tattalin arziki a Faransa da ma sauran kasashen da ke amfani da kudin Euro.