Japan za ta samar da maganin gwaji na Ebola

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hukumar lafiya ta Duniya ta ce za ta amince a yi amfani da maganin da ake gwajinsa, amma da wasu sharudda

Gwamnatin kasar Japan ta ce za ta samar da maganin da ake gwajinsa, domin taimakawa wajen yaki da annobar Ebola a yammacin Afrika idan ana bukatar hakan.

Sai dai Hukumar lafiya ta Duniya ba ta amince da maganin na T-705 a hukumance ba, kuma babu tabbacin ko zai yi aiki wajen warkar da masu cutar Ebola.

Amma wani kakakin kamfanin hada magunguna na Toyoma Chemical ya ce yanayin cutar Ebola da kwayoyin cutar mura na kama da juna, don haka maganin zai yi aiki.

Kawo yanzu dai babu takamaimai maganin cutar ta Ebola, sai dai an samu nasarar warkar da wasu Amurkawa biyu da suka kamu da cutar da maganin Zmapp da ake gwajinsa.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba