An kai hari kan sansanin soji a Madagali

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Ana samun rahotanni masu karo da juna kan wanda ya sa dokar ta-baci a garin, Boko-Haram ko gwamnati

Rahotanni na cewa wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kai hari a kan caji ofis din 'yan sanda da sansanin soji a garin Madagali da ke jihar Adamawa.

Wani mazaunin garin ya shaida wa BBC cewa da safiyar ranar Litinin sun ji karar harbe-harbe da kuma kabbara.

Maharan a cewar rahotanni sun bai wa mazauna garin zabi ko su zauna ko kuma su fice.

Bayanai na nuna cewa mutanen garin da ke zaune cikin gidajensu na cikin zullumi, inda suka ce sun fara fuskantar matsalar abinci.