Boko Haram: Musayar wuta a Gamboru

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Kawo yanzu babu bayanai na asarar rayuka ko jikkata daga bangarorin biyu

Rahotanni daga garin Gamboru a jihar Borno na cewa an yi musayar wuta tsakanin wasu 'yan bindiga da kuma jami'an tsaron Najeriya.

Wani mazaunin garin Gamborun da ya tsallaka zuwa cikin kasar Kamaru ya ce wadanda ake zargin 'yan Boko Haram ne sun shiga garin a motoci da kan babura da safiyar ranar Litinin.

Mutumin ya bayyana wa BBC cewa sun ji karar harbe-harbe da kone-kone da kuma fashewar wasu abubuwa a yayin da suke tsere wa daga garin.

Inda ya kara da cewa jami'an tsaron sun kwashe tsawon sa'oi biyu ko fiye suna musayar wuta da maharan, kuma akwai alamun Maharan sun ja da baya a lokacin artabun.

A halin yanzu mafi yawa daga mazauna garin sun tsere zuwa garin Fotokol da ke jamhuriyar Kamaru.

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba