'Ba gudu Sojojin Najeriya suka yi ba'

Sojojin Nijeriya Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sojojin Nijeriya

A Nijeriya, hedkwatar rundunar sojin kasar ta musanta ikirarin da ake yi cewa kimanin sojojin Nijeriya 500 sun tsere zuwa cikin kasar Kamaru domin neman mafaka a lokacin da suka yi wata arangama da 'yan kungiyar Boko Haram a wasu yankunan da ke kan iyakar Najeriyar da Kamaru.

Hedkwatar tsaron Najeriyar ta ce, dabarar yaki ce ta sa sojojin shiga Kamaru, kuma yanzu haka suna hanyar komawar gida.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun bayanai masu sabawa da juna game da halin da ake ciki a garin Madagali dake Jihar Adamawa, tun bayan da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai hari a karshen mako.