Boko Haram: Sojojin Nigeria sun tsere

Sojojin Najeriya sun sha korafin rashin ingantattun kayan aiki
Bayanan hoto,

Sojojin Najeriya sun sha korafin rashin ingantattun kayan aiki

Mai magana da yawun rundunar sojin Kamaru, Kanal Didier Badjek, ya tabbatar da cewa wasu jami'an tsaron Najeriya 480 sun ketara kan iyaka zuwa cikin Kamaru.

Hakan ya biyo bayan fafatawar da Sojojin Najeriyar suka yi da wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne a garin Banki da ke bakin iyaka da Kamaru a ranar Lahadi.

Kakakin sojin Kamarun ya shaida wa BBC cewa an karbe makaman jami'an tsaron na Najeriya, inda aka dauke su zuwa yankuna daban-daban na garin Marwa.

Wani Mazaunin garin Gamboru ya ce ya ga rukunin wasu jami'an tsaro kimanin 50 akasarinsu 'yan sanda, a lokacin da suke tsallaka iyaka zuwa Kamaru.