Satar bayanai ya dakatar da PlayStation

Hakkin mallakar hoto AFP

Masu satar bayanai sun dakatar da hanyar samun wasan kwamfuta na PlayStation na kamfanin Sony bayan yi masa kutse.

Lamarin da faru a ranar Lahadi ana kallonsa ne a matsayin wani kamfe na adawa da wasannin kwamfuta.

A wani bayani da ya wallafa a shafinsa, Sony ya ce ba a shiga bangaren adana bayanansa ba.

Wasan kwamufuta na XBox na kai tsaye mallakin kamfanin Microsoft da Battle.net na Blizzard da kuma wasannin Grinding Gear na daga cikin wasaannin da aka kai wa harin ta intanet.

Hakan ya zo ne daidai da sauya akalar wani jirgin saman Amurka wanda ke dauke da wani babban jami'in Sony sakamakon jita-jitar saka Bam.

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library

Shugaban sashen wasannin intanet na Sony, John Smedley ya yi bayanai a shafinsa na twitter game yunkurin kamfanin na yaki da satar bayanai na DDoS, kafin ya bayyana cewa zai hau jirgin.

Masu ikirarin rufe shafin wasan kwamfutar na PlayStation sun aika da sakon tweeter inda suka bayyana cewa akwai barazanar tsaro a tattare da jirgin.

'Shawo kan matsalar'

A shafin intanet na rubuta bayanai na Sony, kamfanin ya ce "An katse hanyar sadarwar ne saboda harin da aka kai. Ba mu ga wani alamu da ke nuna cewa an samu shiga kundin bayanai ko kuma an kai ga satar bayanan wani ba."

Sony ya ce yana ci gaba da kokarin aiki don gyara wannan matsala tare da fatan dawowar ayyukansa nan ba da dadewa ba.

Sony ya ce Hukumar FBI na gudanar da bincike a kan jita-jitar sa Bam a cikin jirgin da ke dauke da jami'in na Sony, John Smedley, wanda ya kamata ya sauka a filin jirgin San Diego amma aka karkata akalarsa zuwa Arizona.

Hakkin mallakar hoto AP

Masu satar shiga shafin intanet sun sha yin kutse a hanyar intanet na wasan PlayStation na Sony da ke da mahalarta miliyan 52 ciki har da wata barazanar tsaro a shekara ta 2011.