Anya za a ci galaba kan Boko Haram ?

Hakkin mallakar hoto AFP PHOTO BOKO HARAM
Image caption Abubakar Shekau ya ce sun kafa daular musulunci

Lamarun da ke faruwa a yankin arewa maso gabashin Nigeria a cikin wannan watan sun kara jefa fargaba a tsakanin al'ummar kasar a kan ko dakarun Nigeria za su iya cin galaba a kan 'yan Boko Haram.

Tun bayan da mayakan Kungiyar Boko Haram suka mamaye garin Gwoza a jihar Borno a farkon wannan watan, ake samun rahotanni kan karin wasu yankuna na Nigeria da 'yan kungiyar suka karbe iko da su.

Wasu rahotanni sun ce yanzu haka 'yan Boko Haram din ne ke iko da garin Liman Kara inda mayakan kungiyar suka kwace makarantar horas da 'yan sanda.

Garuruwa na baya bayan nan da mayakan kungiyar suka mamaye dai sun hada da Gamborun Gala a jihar Borno da garin Buni Yadi a jihar Yobe.

'Sojoji sun tsere'

A daidai lokacin da 'yan Boko Haram din ke nuna alamun samun nasara a kan jami'an tsaron Nigeria, sai aka samu rahoton wasu dakarun kasar su kusan 500 sun tsere zuwa jamhuriyar Kamaru bayan gumurzu da 'yan Boko Haram.

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Dakarun Nigeria na ikirarin samun galaba a kan Boko Haram

Daga bisani rundunar sojin Nigeria ta ce ja da baya ga rago ba tsoro ba ne, don haka dabarar yaki ce ta sa zaratan nata rugawa cikin Kamaru.

Dr Jibrin Ibrahim, wani mai sharhi kan al'amurran yau da kullum ya shaidawa BBC cewa, tilas sai gwamnatin Nigeria da jami'an tsaron kasar sun daina musanta cewa wasu yankunan kasar na fadawa hannun Boko Haram kafin a iya kawo karshen wannan matsala.

Ministan yada labaran Nigeria, Labaran Maku ya jaddada cewar "babu wani bangare na yankin Najeriya da zai zama wani wajen gwajin kafa daular 'yan ta'adda a yammacin Afrika, za mu ci gaba da kare mutunci da 'yancin Nigeria, mun gamsu da karfin ikon sojojin Nigeria wajen kare kan iyakokin Nigeria."

'Gudun Hijira'

Sakamakon rikicin Boko Haram, dubban 'yan Nigeria sun tsallaka zuwa makwabtan kasashen domin kaucewa fadawa cikin yanayin marar tabbas da yankin arewa maso gabashin kasar ya fada ciki.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Matan da kananan yara a wata makaranta bayan rikicin Boko Haram ya raba su da muhallinsu

Hukumomi a Nigeria sun ce rikicin Boko Haram ya raba mutane fiye da dubu 650 da muhallansu a yayinda adadin ke karuwa saboda kungiyar na zafafa kai hare-hare.

Alkaluman da aka fitar sun nuna cewar dubban mutane ne suka rasa rayukansu a wannan shekarar kadai, a yayinda wasu dubban suka shiga wani yanayi na galabaita sakamakon yadda rikicin ya kara muni.

'Daliban Chibok'

Fiye da watanni hudu kenan da 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata dalibai sama da 200 a makarantarsu da ke Chibok a jihar Borno.

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya ce ba za su saki 'yan matan ba, har sai an sako musu mayakansu da gwamnatin Nigeria ke tsare da su.

Hakkin mallakar hoto AFP BOKO HARAM
Image caption 'Yan civilian JTF da 'yan Boko Haram suka kama

Kasashen duniya sun sa hannu a yunkurin ceto 'yan matan amma kawo yanzu babu cikakkun bayanai game da inda aka kwana a kokarin kubutar da 'yan matan.

Yanayin da ake ciki a wasu jihohin arewa maso gabashin Nigeria musamman jihar Borno da Yobe, ya sa masu sharhi a kasar ke ganin cewar idan har gwamnatin kasar ba ta tashi tsaye ba, to ikirarin Abubakar Shekau na saka Gwoza cikin daular Musulunci na gab da zamowa gaskiya.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Jonathan ya yi alkawarin ceto 'yan matan da ke hannun Boko Haram